Rundunar Yan Sanda ta gudanar da babban taron tsaro a jihar Zamfara

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara State, Ahmad Muhammad Bello, ya kai ziyarar aiki ta yini guda zuwa Gundumar Mada da ke Ƙaramar Hukumar Gusau, inda ya jagoranci wani muhimmin taron tsaro na manyan masu ruwa da tsaki kan kalubalen tsaro da ke addabar yankin.

A cewar DSP Yazid Abubakar, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ziyarar na da nufin gano hanyoyin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro da ke fuskantar Mada da kewaye.
A yayin ziyarar, al’ummar Mada sun tarɓi Kwamishinan cikin girmamawa ƙarƙashin jagorancin Hakimin yankin, Alhaji Magaji Bashir Magaji (Uban Ƙasan Mada).

Hakimin tare da mambobin fadarsa sun yaba da shugabancin Kwamishinan ‘Yan Sanda da kuma ƙoƙarin rundunar ‘yan sanda na haɗin gwiwa da mafarauta, jami’an tsaron al’umma (CPG) da kuma ‘yan banga wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Haka kuma, Shugaban Ƙaramar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, ya jinjinawa ƙoƙarin rundunar wajen yaƙi da laifuka da masu aikata su.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments