Kotu ta sami wani Dan Majalisar dattawa da laifin safarar sassan jikin mutane

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam.

Shari’ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun.

Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda.

Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25.

Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments