Masana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da takaddamar da ta kaure tsakanin Najeriya da wasu ƙasashen yamma, ciki har da Amurka game da fargabar harin ta’addanci a Abuja.
A farkon wannan makon ne Amurka ta gargaɗi ‘yan ƙasarta cewa da yiwuwar a kai harin ta’addanci a kan babban birnin Najeriyar.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta, tana cewa babu gaskiya a cikin maganar.
Amma daga bisani wasu ƙasashen yammacin duniyar kusan biyar duka sun gargadi mutanensu da su kwana cikin shirin.
Masana harkokin tsaro irinsu Barista Bulama Bukarti da Kabiru Adamu na ganin cewa akwai bukatar mahukuntan Najeriya su dau gargaɗin wadannan kasashen ketare gudun kar a makara.
Masanan na da ra’ayin cewa wannan lokaci ba na ce-ce-ku-ce ba ne, da batun da gwamnatin Najeriya ke yi cewa ana kambama batutuwan da suka shafi tsaron kasarta.
Barista Bulama Bukarti na cibiyar bincike ta Tony Blair da ke Birtaniya ya ce wadannan kasashen da suka ba da gargadi na samun bayanan sirri da suka saba tattarawa kan kungiyoyi ta’addanci.
Masanan dai na ganin cewa bai kamata mahukuntan Najeriya su yi biris da wannan gargaɗi ba, ko sanya siyasa a ciki saboda ankarar da mutum ba laifi bane.
A karshe Masana na da ra’ayin cewa idan aka ci gaba da siyasatar da wannan batu, nan gaba idan Amurka da ƙawayenta suka samu irin wadannan bayanai to za su rufe bakinsu, su ƙi sanar da gwamnatin Najeriya.