Rahotanni Na nuni da cewa yanzu haka Fulani sun fito da wani salo na kwacewa mutane kudade su
Wani bawan Allah da Allah ya kubutar da shi daga wannan sabon makirci da Fulanin suke amfani dashi yace, yana kan hanyar sa ta zuwa kano daga jihar Bauchi motar Sa ta sami matsala sai aka yi yi masa kwatancen inda zai sami mai gyara kuma a take ya nemi mai mashin din da zai kai shi inda zai dauko bakaniken.
Bayan ya Sami wani Bafulatani mai Achaba ya dauke shi, shine yake cewa da shi “Naga alama kai mutumin kirki ne kuma da ganin ka Baza kayi zalinci ba.
Ya ci gaba da cewa ” akwai kudi da muka stint da ya yana kuma muna so a canza mana su amma ba zamu Iya zuwa da kan mu ba saboda Bama so a cuce mu ko kuma yan sanda su kama mu.
“Amma tunda Naga alama kai mutumin kirki ne kazo na hada ka da ya yana sai ka canji kudin bisa gaskiya.
A take mutumin yace ni damuwa ta yanzu na sami bakanike ne ba wannan maganar taka ba sai dai in baka lambar waya in na koma gida mayi waya a take ya yarda.
Sai bayan da ya dawo gida suka kira shi suka ce suna jiran sa ya zo ya canji kudin.
Amma daga karshe da yaki sai suka kama zagin sa suna cewa Allah ya taimake shi bai je musu da kudaden ba.