Kasar Sin na kara fadada kafa turakun samar da nau’o’in makamashi da ake iya sabunta amfani da su, tun daga farkon shekarar nan, yayin da mahukuntan kasar ke yunkurin wanzar da ci gaba, ba tare da gurbata muhalli ba.
Alkaluman hukumar kula da makamashi ta kasar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Oktoba da ya shude, Sin ta kafa jimillar cibiyoyin samar da lantarki da ya kai kusan kilowatt biliyan 2.5, adadin da ya nuna karuwar kaso 8.3 bisa dari a shekara daya.
Cikin jimillar, adadin lantarki ta karfin iska ya karu da kaso 16.6 bisa dari, daga adadin da ake da shi a bara zuwa kilowatt miliyan 350, yayin da lantarki ta hasken rana ya kai kilowatt miliyan 360, adadin da ya karu da kaso 29.2 bisa dari a shekara.
A bana, kasar Sin na kara azama wajen bunkasa zuba jari a fannin makamashi da ake iya sabuntawa, inda aka gina manyan filaye masu dauke da allunan tattara hasken rana, da turakun samar da lantarki daga iska, musamman a yankunan hamada.