Daga Walid Hari.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alƙawarin samar wa Ukraine ƙarin makaman yaƙi bayan harin Rasha mafi muni kan biranen ƙasar .
Mista Biden ya yi magana da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky inda ya yi alkawarin ci gaba da agazawa kasarsa wajen kare kanta daga hare-haren Rasha.
Mista Zelensky ya ce ko kadan Ukraine ba za ta “yi mana barazana ba, mun kara dunkulewa a matsayin tsintsiya madaurinki daya.”
Kalamansa na zuwa ne bayan harin da Rasha ta kai kan wurare a sassan Ukraine abin da ya halaka kimanin mutum 14.
Ƙasashen G7, mafiya karfin tattalin arziki za su gana ta intanet yau domin tattauna karin hanyoyin taimakawa Ukraine.