Rasha na son kammala samar da jiragen yaƙi masu saukar ungulu na Mi-35 guda goma sha biyu ga Najeriya, kamar yadda wani jami’i ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar, Rian, a wajen taron Rasha da Afirka da ke gudana a birnin St Petersburg.
Dmitry Shugaev, shugaban ma’aikatar tarayya ta Rasha kan fasahar aikin soji, ya ce yarjejeniyar sojan ita ce ta taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da barazanar kungiyoyin ƴan ta’adda da kuma shigar da ƙasar cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya.
He did not specify the number of the combat aircrafts delivered so far or when the delivery will be completed but said “the partners are interested in its completion, we continue to work in this direction”.
Bai bayyana adadin jiragen yaƙin da aka kawo ba zuwa yanzu ko kuma lokacin da za a kammala kawo sauran jiragen ba, amma ya ce “Ƙasashen na sha’awar kammala jigilar jiragen, muna ci gaba da yin aiki ta wannan fuskar.”
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ce Najeriya za ta haɗa gwiwa da ƙasar Rasha domin farfaɗo da kamfanin sarrafa aluminium.
Yarjejeniyar dai na daga cikin yarjejeniyoyin da ake sa ran za a ƙulla a yayin taron, wanda shi ne irinsa na biyu bayan da aka yi na farko a shekarar 2019 a birnin Sochi.
Mista Shettima dai yana halartar taron ne tare da wasu shugabannin ƙasashen Afirka.
Tuni dai Rasha ta yi alkawarin samar da hatsi kyauta ga Zimbabwe da wasu ƙasashen Afrika biyar