Dr.mamman dorayi garejin kamilu dhugaban cibiyar hada magungunan gargajiya da likitancin musulinci ya bayyanawa majiyar mu cewar muddin mata basu kauracewa shigar fidda tsiraici da yawan fita gaba gadi ba da shagala a yayin shagulgulan aure ba to aure bazai taba albarka ba kuma rabuwar auran yanzu aka saka dan ba
Ya kara da cewar barin kyawawan al’adun malam bahaushe da akai wadan da basu sabawa shari’a ba shine yasa aljanu suke makalewa a jikin bi’adama musamman ma mata
Daga B.imam
Al’adun kuwa sune a zamanin baya iyaye da kakanni sukan ce a guci fita da garjin rana ma’ana yayin da rana da kwalle sukan killace yaran su kanana da zarar magariba ta doso
Ya kara da bayyana irin zafin sha’awar da jinsin Aljanu keda shi wadda tafi ta bi’adama sannan kuma su matan su na al’janu basa birge su sabida rashin kyan da Allah ya halicce su dashi
Ya shawarci samarin da suka daura damarar aure dasu nutsu su nemi macen da Annabin rahama ya bada shawara a nema wato mai addini addinin kuwa bawai ana nufin duk wadda ka kani kulkum akan hanyar makarantar islamiyya ba ba kuma mai duk wadda take yawan ibada ba mai addinin da ake nufi anan itace wadda zuciyar ta ta cika da tsoron Allah
A karshe yace duk inda kaje neman aure kaga za’a saka ka sauka daga kan koyarwar addini a neman auran da zaman auran to ka canza sheka dumin cewar duk kyan da wadda ka kyalla ka gani tabbata akwai makwafin ta mai tsoron Allah.