*Ina neman Afuwa ga duk wanda na batawa Hafizu Kawu*
Dan majalisar Tarayya Mai wakiltar karamar hukumar Tarauni a Majalisar kasa Hafizu Kawu Tarauni, yace lokaci yayi da Al’umma zasu fahimci cancantar wanda ya kamata ya wakilcesu a Majalisar kasa.
Hafizu Kawu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai, yace a tsawon shekarun da suka gabata ta wakilcinsa a Majalisa ya samar da ayyukan raya kasa daban daban a yankinsa, ta fuskar samawa matasa ayyukan yi da bangaren ilimi da koyar da sana’oi da bada jari.
Hafiz Kawu yace akwai wasu manyan ayyukan nanan tafe kafin karshen wannan wa’adin ,musamman ga yankunan da ayyukan basu je gare su ba.
Hafizu Kawu yayi kira ga daukacin Al’ummar Tarauni da su sake bashi dama a zabe Mai zuwa inda zaici gaba da kawowa yankin kabakin arkizi
Kazalika yaja hankalin matasa da su guji siyasar daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi,wanda hakan ke maidasu baya wajen inganta cigaban rayuwarsu.
Ya kara da cewar duba da rawar da mata ke takawa a sha’anin zabuka hakan tasa yayi masu tsari na musamman da zai tallafi rayuwarsu tare da cigaba da samar masu da jari domin dogaro da kai.
Daganan Dan majalisar yayi addu’ar dorewar zaman lafiya a jihar kano dama kasa baki daya tare da neman afuwar duk wani wanda yake ganin an bata masa domin cigaban jam’iyyar APC a kakar zabe Mai zuwa