Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bincike Kan Kamfanonin Rancen “Sharp Sharp” Kan Zargin Keta Sirrin Bayanai

Gwamnatin Tarayya ta ce tana gudanar da bincike kan ayyukan wasu kamfanonin bayar da rance na “sharp sharp” bisa zargin keta dokokin kare sirrin bayanan kwastomomi.

Kwamishinan Kasa na Nigeria Data Protection Commission (NDPC), Mista Vincent Olatunji, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Talata.

NAN ta ruwaito cewa kamfanonin rancen “sharp sharp”, wadanda ake kira loan sharks a wasu wurare, kamfanoni ne masu zaman kansu da ba su da cikakken tsari na doka. Suna bayar da rance cikin gaggawa ga masu nema, kuma a wasu lokuta har ga wadanda ba su nema ba, ba tare da bukatar jingina (collateral) ba.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments