An bayyana ‘yan ta’adda sun kashe akalla mutane 14500 tare da tilasta wa miliyan biyar da 500,000 tserewa daga gidajensu a cikin shekaru hudu da suka gabata.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban ECOWAS mai barin gado, Jean-Claude Kassi Brou, a yayin mika ragamar shugabancin kungiyar ga sabon magajinsa, Dr. Omar Alieu Touray a Abuja babban birnin Najeriya.
Shugaban mai barin gado ya shawarci Touray da ya zage dantse wajen yaki da yaduwar ayyukan ta’addanci a yankin kasashen Yammacin Afrika.
A cewarsa, tabarbarewar tsaro ta yi matukar illa ga yankin Sahel, inda lamarin ya shafi kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma arewa maso gabashin Najeriya, yayin da a baya-bayan nan ta’addancin ya karu izuwa kasahen Cote d’Ivoire da Benin da Togo da ke gabar ruwa.
‘Yan ta’addan dai da ‘yan bindiga sun jefa kasashen Sahel cikin zaman makoki, ganin yadda suka yi wa kimanin mutane 14500 kisan gilla, tare da haifar da barazana ga zaman lafiyar al’ummomin da ke rayuwa a karkara, baya ga tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa gidajensu inji Brou.
Kazalika Shugaban mai barin gado ya ce, ECOWAS ta yi bakin-kokarinta wajen ganin ta tallafa wa mutanen da rikicin ta’addancin ya mayar da su ‘yan gudun hijirar karfi da yaji.