Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya musanta neman izinin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ficewa daga jam’iyyar APC, Saboda hada musulmi da musulmi a takarar shugaban kasa.
Osinbajo ya ce wata takarda da akai ta yada ta, na cewa ya nemi Buhari ya ba shi damar ficewa daga APC ba daga gare shi take ba.
Takardar mai kwanan watan Yuni 24, 2022 mai lamba SH/VP/605/2./0 mai take ‘Neman Izinin ficewa daga APC,’ ya lissafa matsalolin da wasu dalilan da suka sa ya yanke hukuncin a cikin takarar.
Da yake mayar da martani, Osinbajo, ta bakin mai magana da yawun sa, Laolu Akande, ya bayyana takardar a matsayin ta bogi kuma soki burutsu ce
Akande ya ce Osinbajo ba zai taba yi irin wannan rubutu ba mai cike da kurakurai.
“A ina ku ka samo wannan takarda ? Wa ya baku? don guje wa shakku, waccen takardar bata da alaka ta kusa ko ta nesa ga mataimakin shugaban kasa “ inji shi