A wata sanarwa da ofishin babban lauyan gwamnatin Amurka ta fitar ta ce, ana tuhumar Chidozie Collins Obasi mai shekaru 29 kan aikata laifuka da dama da suka hada da damfara ta hanyar amfani da sakwannin yanar gizo.
A farko-farkon barkewar annobar Covid-19 , Obasi ya yi ta sayar wa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na Amurka na’urar numfashi ta bogi, kafin daga bisani ya saci bayanan wani Ba’amurike, inda ya yi ta karbar kudaden rage radadin cutar Covid-19 da sunansa.
Hukumomin Amurka sun ce, Obasi ba shi kadai ba ne yake aikin damfarar domin kuwa yana da wasu mataimaka a kasar Canada, amma daga Najeriya yake gudanar da na shi ayyukan na damfarar.
Mudddin dai FBI ta yi nasarar cafke shi, Obasi ka iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 621 da kuma cin sa tarar Dala miliyan 5 da dubu 750.
Kazalika hukumomin na Amurka za su tilasta masa maido da daukacin kudaden da ya sace da suka zarta Dala miliyan 31.