Dantakarar Shugabancin kungiyar kasuwar singa kuma, Shugaban kungiyar Kwankwasiyya ta kasuwar singa,Alh Mutari Mohammed Liti Kwasamgwami, ya jaddada kudirinsa na kawo managartan shirye-shirye da za su bunkasa harkokin kasuwanci Alummar dake kasuwanci a cikin kasuwar ta Singa.
Muntari Mohammed kwasamgwami,ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai dangane da yadda Alummar kasuwar suke ta kiraye-kirayen ya fito domin Shugabantar kungiyar kasuwar singa.
Yace, duba da kiraye-kirayen da alummar kasuwar suke yi masa ya sanya ya ga dacewar ya fito domin daukar wannan dauyi na kawo gyara-gyare da bunkasa harkokin kasuwanci da ci gaban matasa da farfado da tattalin arzikin kasuwanci a jihar kano da kasuwar singa.
Shugaban kungiyar ya sha Alwashin hada kai da Gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamnan kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf na Samar da magudanan Ruwa a kasuwar singa domin kaucewa ambaliyar ruwa da kuma, taimakawa Yandako saboda wahalar da suke saman Kansu a lokacin Damina.
Muntari Kwasmgwami ya kuma bayyana cewa, Shugabancinsa zai nemi hadin kan Dattawan kasuwar singa da sauran manyan Yankasuwa da kamfanoni manya domin su zo su hada hannu da kungiyar kasuwar wajen ganin an inganta harkokin kasuwanci a kasuwar ta Singa.
Shugaban kungiyar kwankwasiyyar dake kasuwar singa, Ya bukaci hadin kan alumma manya yara da Dattawan wannan kasuwa da sauran Alummar dake kasuwanci a lungu da sako na kasuwar singa da su marawa wannan Tafiya tasa goyan baya yadda ya kamata domin cimma nasarar da aka sanya a gaba.
Ya kuma bayyana cewa, Shugabancinsa a kasuwar singa zai taka mahimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin Gwamnati mai ci da Aniyar jagoran Kwankwasiyya Dr.Rabiu Musa Kwankwaso na zama Shugaban kasa a nan gaba yace, a shirye Alummar dake kasuwanci a Kasuwar su ci gaba da marawa Gwamnatin jihar kano baya wajen ganin an inganta rayuwar alumma da ciyar da kasuwanci gaba.
Ibrahim sani gama pyramid radio.