Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada Ambasada Mohammed Mohammed a matsayin sabon shugaban hukumar tsaron kasa ta NIA, ya yin da ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Daraktan hukumar DSS.
Ambasada Mohammed ya fara aiki ne a shekarar 1995 inda ya rike mukamai daban daban cikin su harda shugabancin ofishin jakadancin Najeriya a Libya, baya ga aiki a kasashen Koriya ta Arewa da Pakistan da Sudan da kuma fadar shugaban kasa.
Shi kuwa Ajayi ya fara aiki ne tun daga matakin farko a hukumar DSS har zuwa lokacin da ya kai matakin mataimakin Darakta baya ga shugabancin hukumar a jihohin Bauchi da Enugu da Bayelsa da Rivers da kuma Kogi.