Biyo bayan Dakar da aikin titin Kano zuwa Kaduna abune mai kyau mahukunta daga wadannan jihohi subi matakan da suka Dace wajen magance matsalar da aka danganta da sanadiyar dakatar da aikin.
Tashin farko yadace lamba daya na wadannan jihohin su bibiyi matsalar domin su yi aiki a kan ta
Za a iya ya cewa wannan aiki yana cikin sahunsa gaba da jihohin biyu zasu amfana tun kafa gwamnatin Shugaba Buhari cikin shekara bakwai da watanni.
Kamar ita jihar Kaduna a iya cewa ta amfana da bude tashar jirgin kasa da kaddamar da Layin dogo mai tafiya Kaduna zuwa Abuja wanda dama gwamnati Goodluck Jonathan ta samar kafin ta shude.
Ita kuwa jihar Kano sai alkawura da ba zasu samu ba kamar na tashar jirgin kasa ta sauke kwantenoni wadda akace zata dangana zuwa Lagos da aka samar da filin kuma akaki fara shimfida kayan aiki sai kuma Layin Dogo wanda zai tashi daga Kano zuwa marauding Shima shuru kake ji wait Malam yaci shuwa.
Kamar yadda mai wasikar ya rubuta yace “hakan a lokuta da dama ana danganta shi da sakacin mahukunta na jihohin Hausawa kuma abune da yadace ace suna koyi da jihohin yarbawa ka na iya muradi”