Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun yi ram da wani matashi da ake zargi da zama ‘dan damfara a kan hanyarsa ta zuwa Yola
An kama matashin mai suna Joseph Nwakibe da katinan ATM guda 10 na bankuna daban-daban wadanda suke damfarar mutane da su
An gano cewa suna hawa layi kamar kwastomin bankin yayin da suke musayar kati ga wadanda suka nemi a taimake su sannan su hada da lambar katin don damfara
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta damke wani da ake zargi da zama ‘dan damfara mai suna Joseph Nwakibe wanda wani abokinsa mai suna Obinna Ajima ya gayyata a Yola domin aiwatar da lamurran ta’addanci.
An bayyana hakan ne a wata takarda da rundunar ‘yan sandan suka fitar a ranar Juma’a wacce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Yahaya.