A madadin ma’aikatan da shugabancin aksammedia jaridar dake yada labarai ta kafar yanar gizo sunyi tir da cin zarafin da wani jami’in ɗan sanda ya yiwa ma’aikacin premier radio a lokacin da ya ke bakin aiki.
Ɗan jaridar mai suna Muhammad Bello Dabai ya fuskanci Mari da Duka da Zagi tare kuma da Tursasawa daga gurin wani jami’in ɗan sanda a lokacin da ya ke ƙoƙarin ɗaukar hoto domin haɗa labari kamar yadda manajan sashen labarai na gidan rediyon Premier Malam Mukhtar Yahaya Usman ya sanar da manema labarai.
Dan jarida wakiline na al’umma masu karfi da marasa karfi
Finance Bill: Dangote, 171 firms may lose N2.4tn tax waivers
Tun da fari dai lamarin ya faru ne bayan da wani mutum da ya ke fuskantar tuhuma a hannun jami’an yansanda ya kuɓuce musu a lokacin da ake tafe da shi zuwa Abdullahi Wase da ke birnin Kano domin a duba lafiyarsa.
Bisa yadda lamarin ya faru tun bayan da wanda ake tuhuma ɗin ya kuɓuce sai ya biyo ta gaban gidan Rediyon Premier inda a nan ne mutane su ka cimma masa kafin daga bisani jami’an ƴan sandan su ka karaso su tafi da shi.
Hakazalika Mukhtar Yahaya ya ce bayan da jami’an ƴan sandan su ka kama wanda su ke tuhumar daga nan ne Muhammad Bello Dabai ya ɗakko waya domin ɗaukar hoton abin da ya faru, inda a nan ne wani jami’in ɗan sandan ya fara zagi tare da marin ɗan jaridar duk da cewa ya gabatar da kan sa tare da nuna katin shaidar aiki.
Bayan shan mari da duka Jami’in ɗan sandan ya tursasa Muhammad Bello Dabai shiga cikin motarsu tare da kwantar da shi a ƙasan motar, inda su ka tafi da shi caji ofis su ka tsare shi na wani lokaci.
Ana dai yawan zargin jami’an tsaron ƙasar nan musamman yan sanda da keta hakkokin ƴan adam. Domin ko a baya – bayan nan sai da ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce ana samun yawaitar kai wa ‘yan jaridar Najeriya samame tare da tsorata su, abin da yasa ‘yan jaridar ke aiki cikin yanayi na tsoro da firgici.