Rundunar sojin Najeriya ta kama mai kaiwa yan Boko Haram kayayyaki

Dakarun sojojin Nijeriya sun sami nasarar kama wani dan Boko haram tsagin ISWAP daya kware a fannin kerawa da gyaran bindiga a kauyen Gorom dake karamar hukumar Monguno a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata takardar sanarwa da shalkwatar rundunar ta aikewa PRNigeria mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran rundunar sojin Nijeriya Manjo Janar Musa Danmadami,

Sanarwar tace a ranar 26 ga watan satumba zuwa 3 ga watan Oktoban wannan shekara dakarun sojojin sun sami nasara kama shi, dauke da gidan shirya alburushi guda 300 babu alburushin a ciki, wanda ake zargin yin amfanin dasu wajen shirya alburushin mai tsayin 7.62mm.

An dai zargi kwararren makerin bindigar ne da kasancewa guda cikin masu bada bayanan sirri ga mayakan Boko Haram tsagin ISWAP a wurare daban-daban, haka kuma rundunar ta sami nasarar cito ‘yan matan Chibok 2 da suka hadar da Yana Pogu da rejoice Senki wanda ke da lamaba ta 19 da 70 cikin jerin jadawalin ‘yan matan Chibok da aka sace da ‘ya’yan s a kauyen Bula Davo dake karamar hukumar Bama da kauyen Kawur dake Karamar Hukumar kunduga a jihar Borno gami da wasu wadanda aka sace su 12.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments