Kamfanin man fetur na NNPC ya tabbatar da cewa ya ƙara kuɗin litar mai a ƙasar.
A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na twitter, kamfanin ya ce ya yi ƙarin farashin domin yin daidai da halin da ake ciki.
Kuma ya roƙi afuwa kan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa.
Hakan dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar, a lokacin rantsar da shi cewa gwamnati ta dakatar da tallafin.
Tun bayan furucin sabon shugaban ƙasar ne aka fara ganin dogayen layuka a gidajen mai, yayin da kowane gidan mai ke sayar da man a farashi daban-daban.
Ita ma, Ƙungiyar Dillalan Man Fetur masu Zaman Kansu ta Najeriya (IPMAN), ta fitar da sabon farashin da gidajen mai za su rinƙa sayar da litar mai a faɗin ƙasar.
A cewar ƙungiyar, ta ɗauki matakin ne bayan da Kamfanin Man Fetur na Ƙasar (NNPC) ya miƙa mata nasa sabon farashin.
A zantawar sa Shugaban ƙungiyar reshen Arewa, Bashir Ɗanmalan wanda ya tabbatar wa BBC da ƙarin, ya ce yanzu farashin zai kama ne daga naira 500 zuwa 600, dangane da yankin ƙasar.
Dama dai farashin man fetur ya tashi a sassa daban-daban na ƙasar tun bayan furucin sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinu, wanda ya ce “Tallafin man fetur ya tafi.”
An rinƙa samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai, inda farashin lita ya rinƙa tashi babu ƙaƙautawa
Bashir Ɗanmallam ya ce kamfanin NNPC ya ce zai rinka sayar wa dillalan litar man fetur a kan naira 476 a Legas, a Warri kuma za su saya a kan naira 483.90, a Fatakwal kuma da Calabar za asayar musu a kan naira 487.70.
Ya kuma ce suna ƙarin farashin da ƙungiyar ta yi a yanzu na wucin-gadi ne, inda suke sa ran fitar da wani farashin bayan tattaunawa da sauran ƙungiyoyin da ke da ruwa da tsaki a harkar ta mai.
Ya ce a yanzu an kasuwa ne za su rina tantance farashin sayar da man fetur.