Kocin Manchester United Erik ten Hag yana son sayar da mai tsaron gida na Ingila Harry Maguire a kakar wasa mai zuwa, kuma kulob din ka iya karbar fam miliyan 80 kan dan wasan mai shekara 29. (Guardian)
Dan wasan gaba na Netherland Memphis Depay, mai shekaru 28, wanda ake kyautata zaton zai koma taka leda Tottenham ko tsohon kulob dinsa Manchester United, yana kuma son barin Barcelona a kyauta idan an bude kasuwar ‘yan wasa a watan Junairu mai zuwa. (Mundo Deportivo via Express)
Mai kai hari na Faransa Kylian Mbappe, dan shekara 23, ya ce yana son sunan shi ya shiga kundin tarihi a Paris St-Germain maimakon komawa wata kungiya domin cin kofin Champions League. (Sports Illustrated)
Manajan Atletico Madrid Diego Simeone ya ce ya na son dauko mi kai hari na Portugal Joao Felix dan shekara 23, duk da cewa dan wasan na da alaka da Paris St-Germain. (Fichajes)
Chelsea ta karbi bakuncin dan wasan Palmeiras kuma mai kai hari Endrick dan shekara 16, tare da iyalansa, lokacin atisayen da suka yi a kokarin lallasa Paris St-Germain da kokarin daukar dan wasan Brazil da Real Madrid ke sonyi. (Mail)
Arsenal na shirin dauko dan wasan tsakiya na Belgium da Leicester City Youri Tielemans, mai shekara 25, da dan wasan tsakiya da ke buga wa Brazil da Palmerias Danilo, mai shekara 25 a watan Junairun badi (90 Min)
Newcastle United ta fara zawarcin dan wasan Shakhtar Donetsk kuma na gaban Ukraine Mykhaylo Mudryk, mai shekara 21 wanda ake ganin kamar Arsenal na zawarcinsa.(Football Insider)
Newcastle United z ta saurari tayin dan wasa Matt Ritchie a wtan Junairu, idan kociyanta Magpies y amince da sallama dan wasa Eddie Howe mai shekara 3. (Football Insider)
Wayne Rooney y ace, Roy Keane ba zai amince da dabi’ar dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, a tsohon kulub din shi Manchester United a wannan kakar wasan. (Talksport)