Babban jirgin saman fasinja samfurin C919 da kasar China ta kera, ya Sami takardar shaidar da aka kera shi wanda hakan ke nufin kasar ta China zata cigaba da kera jirgin mai samfurin C919.
Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin (COMAC), wanda ya kera jirgin na C919, ya karbi takardar shaida inganci daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar China (CAAC) dake da ofishi a yankin gabashin kasar.
A shekarar 2017 jirgin saman ya kammala gwajin tashinsa na farko cikin nasara, ya kuma samu irin wannan takardar shaida a karshen watan Satumba, abin da ke nuni da cewa, tsarin na C919, ya dace da mizanin tashi da kuma ka’idoji na muhalli.
A watan Maris din wannan shekara ce, kamfanin jiragen sama na China Eastern Airlines (CEA), ya sanya hannu kan kwangilar sayen jiragen na C919 guda 5, wannan shine farkon kulla kasuwanci tsakanin kamfanonin biyu
Sakataren hukumar CEA Wang Jian, ya bayyana cewa, ana sa ran mikawa kamfanin na CEA jirgin farko a watan Disamba, za kuma a bayar da ragowar jiragen da aka yi oda a cikin shekara 1 ko biyu masu zuwa, bisa tsarin samar da jiragen.
Ana kuma sa ran kamfanin CEA, zai fara harkokin zirga-zirga da jirgin a cikin watanni 6 na farkon shekarar 2023.