Karota basu da ikon karbar kudin Diriving permit in sun kama mai mashin: Barista Bashir Sani Idris.

Karota basu da ikon karbar kudin Diriving permit in sun kama mai mashin: Barista Bashir Sani Idris.

Abdulhamid Isa D Z

An bayyana Hukumar kula da zirga zirgar ababan hawa ta jihar kano (Karota) tana da damar yin amfani da dokar sashi na 16 da ta kafata na shekarar 2012 wajan kama driving permit Amma basu da ikon karbar kudin da suke karba naira 2500.

Daga Abdulhamid Isa D Z

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Barista Bashir Sani Idris A zantawar sa da wakilin Aksammedia, Abdulhamid Isa Durumin Zungura.

Barista yace abin da yake a doka shine idan Karota ta Kama mutum da laifin driving permit zata mika shine ga Hukumar da take da alhakin akan abin daga bisani kuma a kai shi gaban kotu ta hukun ta shi.

Daga karshe Barista Bashir ya bada shawara ga masu ababan hawa da su rika bibiyar doka domin sanin meye suke da yanci meye basu da yanci hakan zai taimaka su rayu cikin yancin kai wanda aka samu Tun daga hanun turawa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments