Alummar Arewa na cigaba da ganin baiken shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yawa suna cewa “Mulkin ya kare, Arewa babu wutar Mambila, babu Ruwan Baro, babu kamfanin Ajaokuta, babu Rijiyoyin Fetur a Bauchi da Gombe, Babu makarantar petroleum training institute ta Kaduna, Babu wutan Zungeru, babu layin dogon Kano-Kaduna, Babu na Lagos-Maiduguri, babu na Kano-Maradi, an kasa gyaran refineries, an kasa gina sabbi duk da alkawarin da suka yi, an kasa gyara sha’anin ilimi, kusan shekara babu karatu a jami’oin mu, an kasa gyara sha’anin lafiya, a yau 12.5kg silindar gas tana N8000+ fetur sai yadda ka samu, man gas (diesel) #790 liter, an bada bashin noma amma ‘yan ta’adda sun hana noman.
Duk inda shanu suke anbi an sace, Mun koma sai mun biya ‘yan ta’adda haraji kamun su barmu mu zauna a garuruwanmu.
A Arewa kowa a tsorace yake, a yau baka san a tsakanin kai ko iyalinka wa za’a fara kamawa ba, sannnan a Maiduguri da arewa maso yamma, mata a aure su da karfi da yaji babu sadaki babu waliyyi.
Arewa ta tashi a tutan babu, ‘yan ta’adda duk sun kwace garuruwa da dazuzzuka.
Textile companies especially Kaduna, Kano, textile etc are still in comatose. Dan Arewa bisa Mulki bai gyara textile industries ba a shekara bakwai da Kari, sai kokarin rufe boda da hana shigowa da tufafin gwanjo.
Allah wadan naka ya lalace. Wannan wane irin mulkine?”