Kotun daukaka kara ta tarayya ta amince a kashe mawakin da yayi batanci ga fiyayyen halitta s a w

A cikin watan Agustan shekarar 2020 ne, Kotun Shari’ar Musuluncin ta yanke wa mawakin nan da yayi batanci ga fiyayyen halitta s a w wato Sharif hukuncin kisa ta hanya rataya bisa wasu kalamai da yayi Na batanci ga janibin annabin rahama s a w.

Bayan yanke hukunci a wancan lokacin Mawakin ya daukaka kara domin kalubalantar hukunci da aka yi masa, kuma a cikin watan Nuwamban 2020,  kotun jihar Kano ta yi watsi da hukuncin kisan tare da bada umarnin sake gudanar da shari’ar a gaban Kotun Daukaka kara ta Shari’ar Musulunci.

Sai dai Kotun ta Daukaka Karar Shari’ar Musuluncin ta goyi baayan hukuncin kisan a watan Janairun bara.

Duk da haka dai, lauyoyin da ke kare Sharif ba su yi kasa a guiwa, inda suka sake daukaka kara  tare da neman a yi masa shari’a a kotun da babu ruwanta da addini.

Sai dai a wannan Larabar, Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ita ma ta sake goyon bayan hukuncin kisan kan Sharif a wani zama na mintina 17 da ta yi ta kafar bidiyo.

Alkalin da ya jagoranci zaman, Abubakar Mu’azu Lamido ya ce, daukaka karar ba ta da armashi, a don haka an yi watsi da ita, yanaa kuma mai cewa, Shari’ar Musulunci ba ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba.

Jim kadan da yin batancin a cikin wata wakarsa, fusatattun matasa suka kona gidan iyayen Sharif  tare da gudanar da zanzga-zanga akan titunan birnin Kano.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments