Daga Sadik Lamin Hassan.
Gwamnan jihar katsina HE. Rt. Hon. Aminu Bello Masari Dallatun Katsina ya ce daga yanzu duk wata gwamnatin sa za ta cigaba da sakarwa kananan hukumomi 34 na jihar katsina kudade Kai tsaye domin gudanar da ayyukan raya kasa, da jin kan al’uma .
Gwamna Masari ya bayyana hakan a wajen bikin mika sabbin motocin ofis ga sabbin shuwagabannin kananan hukumomi 34 na jihar katsina, wanda ya gunada a sashen saukar baki na shugaban kasa, da ke cikin Fadar Gwamantin Jihar Katsina.
Haka Kuma gwamnan ya miqa mota kirar siyana ga Kwamitin yakin neman zaben Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Dikko Umar Radda, wadda Mai ba shi shawara na musamman Alh. Bishir Dayyabu Safana ya bayar guddumuwa ga Dantakarar Gwamnan .