Jimillar mutane 1,789 aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna a rabin shekara.

Daga Sadik Lamin Hassan

 

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sacewa tare da yin garkuwa da mutane 1,789 a cikin watanni 6. Gwamnatin jihar ta kuma sanar cewa an kashe ‘yan ta’adda 161 a lokacin musayar wuta da jami’an tsaro a lokutta daban-daban cikin watannin 6.

 

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan shine ya sanar da hakan a lokacin da ya ke gabatar da rahoto kan tsaro na 2022, inda ya ce an kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba su 285.

 

Samuel Aruwan ya ce an kuma sace shanu 1,133 tare da kama mutane 654 da zargin aikata ta’addanci.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments