Amurka za ta karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka 49 da kuma tawagar kungiyar Tarayyar Afirka a birnin Washington domin halartar taron kwanaki uku na Amurka da Afirka da za a fara ranar Laraba mai zuwa.
Gwamnatin Shugaba Joe Biden ta ce tana son yin amfani da taron don “sabunta” dangantaka da nahiyar.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce Amurka ma ba za ta so a ce an bar ta a bayan China da Rasha ba, wadanda tasirinsu a Afirka ke ci gaba da karuwa.
Biden bai gayyaci Burkina Faso, Guinea, Mali da Sudan ba saboda shugabaninsu na soja ne da aka dakatar daga kungiyar A.U. Eritrea, Yammacin Sahara da Somaliland su ma ba za su zo Washington ba, saboda Amurka ba ta da huldar diflomasiyya da su.
Sai dai wasu da ake zargi da take hakkin dan Adam da danniya a siyasance da suka hada da Masar da Habasha da kuma Zimbabwe za su zo taron.
A hirar shi da Muryar Amurka, Parfesa John Stremlau, wani kwararre a fannin harkokin kasashen duniya kuma tsohon jami’in diplomasiyan Amurka a Afrka, ya ce. ” duba, wannan duniyar fa ba ta cike 10 ba, saboda haka dole ne a sasanta, kuma ina tsammanin a wannan lokacin, mataki ne mai kyau don gudanar da taron kolin Afirka…”
Ya kara da cewa, “Akwai tambayoyi da dama amma a ƙarshe yana da mahimmanci shugabanin Afirka su gana da gwamnatin Biden, musamman bayan gwamnatin Trump, wacce ke adawa da Afirka da wariyar launin fata na cikin gida.”
Ya ce wani mutum mai mahimmanci da zai halarci taron shi ne Enoh Abong, darektan hukumar kasuwanci da ci gaban Amurka, wanda Ba’amurke ne kuma dan Najeriya. Yana sa kaimi ga kamfanoni masu zaman kansu na Amurka cikin ayyukan ci gaba.
Wani muhimmin jigo, in ji Stremlau, shi ne Adewole Adeyemo, wanda ya kasance Ba’amurke ɗan asalin Afirka na farko da zai yi aiki a matsayin mataimakin sakatare na baitul malin Amurka.
Stremlau ya ce zuwan Abong da Adeyemo alamu ne masu ƙarfi.
Ya ci gaba da cewa, “Abin tunatarwa ne cewa ‘yan Afirka mazauna kasashen waje suna da mahimmanci ga dimokuradiyyar Amurka, kuma ya zama wajibi ga ‘yan Afirka su shiga amma su yi hakan idan za su iya da murya daya. Don haka ina tsammanin akwai ‘yancin aiki mai ma’ana, amma ya kamata ajanda ya zama tattalin arziki, yanayi, dorewa, wanda shine inda Amurka ta yi alkawura. Yana cikin muradin ‘yan Afirka cewa suna da tsarin dimokiradiyya a Washington. Yana da kyau tunatarwa cewa ‘yan Afirka za su iya yin aiki tare da Amurkawa muddin suna aiki tare da ‘yan China da sauran su.”
Ya ce akwai batutuwa masu amfani da yawa da za a yi magana akai, kamar yadda Amurka ke taimakawa Afirka a fannin lafiya da sauyin yanayi, da sabunta dokar ci gaban Afirka.
“Kuma rage tasirin yakin Ukraine, wanda kamar yadda Martin Kimani, jakadan Majalisar Dinkin Duniya daga Kenya ya yi nuni da cewa, wani hari ne kan tushen da suka kasance ginshikin tsarin kasa da kasa da na kasashen Afirka; daidaiton mulki da mutuncin yanki.”
Stremlau yana sa ran jami’an Biden za su jaddada batun samun shugabanci nagari a Afirka. Ya kuma yi nuni da cewa kundin tsarin mulkin A.U ya nanata kimar dimokuradiyya da zabuka masu inganci.
“Domin biyan bukatun kansu, ya zama wajibi Afirka ta samu duniyar da ba a mulkin kama-karya, amma inda ake yin sulhu da diflomasiyya. Kuma ina ganin za su iya shiga wannan taro karkashin Tarayyar Afirka, tare da yin kira ga dukkan kasashe da su mutunta kimar Yarjejeniya ta Afirka tare da tallafawa ‘yanci ciniki na Afirka. Hakan na nufin idan ‘yan China na son yin aiki a Afirka, bai kamata su rika yin cudanya da harkokin cikin gida na Afirka ba, haka su ma Amurkawa, da ma Rashawa, su ma bai kamata ba. Amma ya kamata akalla su kyale Afirka ta yi zabin dimokradiyya maimakon zabin mulkin kama karya, don amfanin Afirka.”