Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR CNOL ya bukaci sabon kwamishina yan sandan jihar Kano CP Mamman Dauda da ya tabbatar ya tsaya tsayin daka wajen kare lafiya da dukiyoyin al’umma jihar kano.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin sabon kwamishinan yan sandan na jihar Kano CP Mamman Dauda yayin da ya ziyarce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace jihar Kano jiha ce mai al’umma da yawa, yace dole ne sai sabon kwamishinan yan sandan da ma’aikatan sa sun kara himma wajen kula da rayukan al’umma.
Anasa jawabin sabon kwamishinan yan sandan na jihar Kano CP Mamman Dauda ya ce rundunar “yan sandan jihar Kano zata cigaba da kokarin ganin ta kula da harkokin tsoran jihar kano.
Ya kuma bude sabon offishin yan sanda dake kofar kudu a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.
Haka kuma a wani ciganan Mai Martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin shuwagabanin kungiyoyin dalibai jami’oin kasar nan.
Sa Hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano