Shugaban kasar China ya gana da takwaran sa na kasar Masar

Shugaban kasar China  Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Masar, Abdel Fattah al Sisi a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.

Yayin ganawar, Xi ya ce, bisa halin da ake ciki yanzu a duk duniya, da ma shiyyoyi daban-daban na fuskantar manyan yanayin sauye-sauye, Abu mafi  muhimmanci shine  a raya hulda din kasar  Sin da Masar bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoi.

A cewar sa ya dace kasashen biyu su yi kokari tare, don neman cimma burin ginawa al’ummominsu kyakkyawar makoma ta bai daya, ta yadda za’a kara samar da sabon ci gaba, ga dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare ta kowanna fanni.

A nasa bangaren, shugaba Sisi ya ce, ya ziyarci  kasar Sin ne domin  halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da aka saba gudanarwa birnin  Beijing.

Kazalika ya bada shawarwari masu gamsarwa tare da shugaba Xi. Ya ce, ya ziyarci kasar Sin a wancan lokacin ne don goyon bayan kasar, da karfafa dangantaka tare da kasar. Sisi yana da yakinin cewa, a sabon wa’adin aikin shugaba Xi, dangantakar kasashen biyu za ta samu karin ci gaba, kana, kwalliya za ta biya kudin sabulu, wajen karfafa hadin-gwiwarsu a bangaren shawarar “ziri daya da hanya daya”.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments