Hukumar DSS ta ankarar da al’umma cewa akwai shirye-shirye da wasu miyagu su ke yi na kai wa wuraren bauta da filayen wasanni hari a lokutan bukukuwan Salla.
Jaridar Punch tace, an fahimci cewa ana yunkurin kai hare-haren ne a lokuta da kuma kafin bukukuwan babbar sallah.
Mai magana da yawun hukumar DSS ta kasa, Dr. Peter Afunanya ya yi kira ga masu manyan shaguna su kara sa ido a daidai lokacin nan da aka shiga.
Peter Afunanya ya shaida cewa jami’an tsaro masu fararen kaya da dakarun ‘yan sanda da sojoji sun yi nasarar gano wasu makaman IED masu tashi.
Bama-baman da ake shirin tadawa su ka haskawa jami’an tsaro ana niyyar ta’adi.
Afunanya ya bada shawarar cewa jama’a su yi gaggawar ankarar da jami’an tsaro da zarar sun ci karo da wasu mutanen da ba a sani ba.
Hukumar DSS ta na kira da a sa ido kafin bukukuwan Sallah musamman da rahotanni su ka zo cewa ana so a kai hari a dakunan bauta da wuraren shakatawa kafin da bayan bukukuwan.
Hakan ya bayyana ne bayan gano wasu makaman IEDs da ake zargin ‘yan ta’adda sun kafa.
Ana yin kira ga shugabanni da masu kula da wuraren taron jama’a har da kasuwanni, shaguna da sauransu da su sa ido kuma su kai rahoton duk wani motsi ko mutanen da ba a gane kan su ba.