Shugaban Kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya gargadi Kasashen yamma kan cewa su gaggauta shiga yakin da Kasar say take fafatawa da Kasar Rusia.
Zelensky ya bayyana hakan ne a zantawar sa do kafar yada labarai ta BBC, inda yace Yana jiyewa sauran kasashen yamma tsoron cewa Rusia ba zata kyale su ba da zarar ta gama da Kasar say ta Ukraine.
Zelensky cikin rauni yace Yana sa rai Kasar Amurka zata you du Mai yuwuwa wajan ganin ta dakatar da cigaban yakin, kasancewar Kasar sa bata da ikon Kare kanta daga hare-haren da Rusia take kaimata ta sama da kasa a halin da ake ciki.
Kazalika bayan bayyana karayar sa afili yace Yana sa Rai kungiyar NATO da Amurka zasu shiga su dakatar da yakin.
Editor, Hassan Umar Gwammaja