Mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS kuma darektan ofishin hukumar harkokin waje na kwamitin kolin JKS, Wang Yi ya halarci taron tsaro da ya gudana a birnin Munich na kasar Jamus, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.
tare kuma da amsa tambayoyin da aka yi masa.
Wang Yi ya yi tsokacin cewa, yanzu ana mai da hankali matuka kan batun balan balan maras matuki na kasar China da ya shiga samaniyar kasar Amurka bisa kuskure, inda Amurka ta siyasantar da batun. Kasar Sin ta riga ta gayawa Amurka cewa, balan balan din ba na aikin soji ba ne, ya kauce hanyar da yake bi, ya shiga samaniyar Amurka sakamakon kadawar iska, don haka kasar Sin ta bukaci Amurka da ta kai zuciya nesa ta daidaita batun tare da kasar China.
Amma abun bakin ciki shi ne, Amurka ta yi biris da hakikanin abubuwan da suka faru, ta tura jirgin saman yaki, ta harbo balan balan din da ba zai haifar da kalubalentar ba, matakin da Amurka ta dauka ya sabawa yarjejejiyar kasa da kasa, Kuma kasar China ba ta amince da hakan ba, ta riga ta soki lamarin da ma nuna adawa ga Amurka.
Dangane da rikicin kasar Ukraine, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar China ta damu kan rikicin, tana fatan bangarorin da abin ya shafa, za su yi shawarwari domin daidaita batun yadda ya kamata, saboda burin kasar Sin shi ne tabbatar tsaro a Duniya.
Yayin taron tsaron a Munich, Wang Yi ya yi kwarya kwaryar ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, inda ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun balan balan din