Bayan mutuwar Sarauniyar Ingila, yanzu haka mulkin ya koma kan ɗanta magajinta Charles, tsohon Yariman Wales, ba tare da wani bikin naɗin sarautar ba.
Daga Walid Y Hari
Yadda naɗin sarautar zai kasance
A cikin sa’a 24 na farko bayan mutuwar mahaifiyar tasa za a nada shi.
Amma akwai matakai na al’adu da dama da za a aiwatar masa kafin a tabbatar da shi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa
Za a dinga kiransa da Sarki Charles na III.
Wannan ne mataki na farko na zama sabon sarki. Zai iya zaɓa daga cikin sunayensa huɗu – Charles Philip Arthur George.
Ba shi kadaine ne samun sauyin suna ba.
Duk da cewa shi ma mai gadon sarautar ne, Yarima William ba zai zamo Yariman Wales kai tsaye ba. Sai dai, tuni ya karɓi ɗaya tsohuwar sarautar mahaifin nasa ta Duke na Cornwall.
Ita kuma matarsa Catherine za a dinga kiranta da Duchess ta Cornwall.
Matar Charles kuwa, sabon sunanta shi ne Sarauniya Consort – consort ce kalmar da ake amfani da ita wajen kiran matar sarkin da ke kan mulki.