Rahotanni na nuni da cewa ‘yan siyasa, da jami’an tsaro, da ‘yan kasuwa, da rsagerun Neja-Delta da kuma hukumomi ake hada-kai wajen satar arzikin man fetur din kasar nan.
A Wani bincike da jaridar Vanguard ta gudanar a makon da ya gabata, ya fallasa yadda wadannan gungun mutane suke da hannu a badakalar satar danyen mai. Tsagerun Neja-Delta suna sace danyen mai daga bututu a Neja-Delta, yayin da su ma’aikatan gwamnati suke agaza masu ta hanyar tunkudo danyen man.
Akwai kananan tsageru da ke satar danyen mai daga bututun Najeriya, sai su saidawa manyan barayi, su kuma manya suna saida man ga kasashen waje.
Masu wannan danyen aiki sun hada-kai da jami’an tsaro wadanda suke nuna masu yadda za su dauki jirgin man da suka sata domin saidawa barayi a kan teku. Rahoton yace duk jami’in tsaron da yake wannan danyen aiki, yana samun makudan kudi duk wata.
Kamfanoni sun koka da masu aika-aikar Kamfanonin mai kamarsu Shell Petroleum Nigeria Limited, Chevron Nigeria Limited da NNPC sun dade suna kokawa da barnar da bata-gari suke yi a Najeriya. Wani jami’in SPDC, Igo Weli ya nuna cewa babu shakka manya suna cikin barayin man domin talaka ba zai iya mallakar kayan aikin da ake amfani da su
Tun a baya Shugaban bankin United Bank for Africa, Tony Elumelu ya taba cewa Najeriya tana asarar abin da ya kai 95% na arzikin man da da ake da shi ta dalilin barayi.