*Man United ta taka wa Arsenal burki bayan cin wasa biyar a Premier*
Daga Walid Yusuf Hari
Manchester United ta doke Arsenal 3-1 a wasan mako na shida a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.
United ta fara cin kwallo a minti 35 ta hannun Anthony, sabon dan wasan da ta dauka a bana daga Ajax.
Tun a minti na 12 da fara tamaula Gabriel Martinelli ya ci Manchester United kwallo, amma aka soke ta cewar an yi wa Eriksen keta tun farko.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Bukayo Saka ya farke kwallon da aka ci Gunners.
Sai dai kuma minti shida tsakani Marcus Rashford ya kara ta biyu sannan ya ci ta uku da ya sa United ta hada maki ukun da take bukata.
Rabon da Rashford ya ci Arsenal kwallo tun ranar da ya fara yi wa United wasa a cikin watan Fabrairun 2016, kafin wasan Lahadi ya fuskanci Gunners sau 13.
Dan wasan Manchester United, Antony wanda shi ne na 100 daga Brazil da ya koma buga Premier League shi ne na farko daga kasar matashi da ya ci kwallo a wasansa na fari.