Rahotanni sun bayyana cewa mutumin da ya fi kowa kazanta a duniya ya rasu yana shekara 94
Amou Haji wanda dan kasar Iran ne ya rasu ne a ranar Talata 25 ga Oktoba 2022 bayan ya kwashe shekaru 67 bai yi wanka ba.
Abincin da yake ci sun hada da rubabben nama da matattun dabbobi. Yana matukar jin dadin cin bushiya da shan tabarsa ta koko kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Kafin rasuwarsa, hajji ya yi imanin cewa ruwa da sabulu za su sa shi rashin lafiya wanda shi ya sa ya kwashe tsawon wadannan shekaru ba tare da wanka ba.