Alamu na nuna cewa, Ortom ya kullaci Atiku ne tun bayan martanina ga wasu kashe-kashe da suka faru a jihar Benue da ake zargin Fulani makiyaya ne sukayi.
Hakazalika, ya zargi Atiku da yiwa kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, wacce yace kungiyace mai mallakar makamai.
A cewar Ortom: “Ba daidai bane dan takarar shugaban kasa wanda ke neman ya mulki jama’a ya fadi irin wannan abin ba.
Babban kuskure ne. Kuma ma gani nayi bai ma mutunta ni ba ya ganni a matsayin gwamna na jihata.”
Ortom ya kara da cewa “Bana cikin tawagar kamfen dinsa. Mutanen da suka nada a can, ba su da izini na. Don haka ni ina nan ni kadai. Amma ina jira; lokacin da zabe yazo, za mu yi zaben ne a yadda yazo.”
Ortom dai daya ne daga cikin wadanda ke kalubalantar shugabancin jam’iyyar PDP tun bayan kammala zaben fidda gwani da kuma nada Okowa a matsayin abokin takarar Atiku. Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ne ummul-khaba’isin duk wata fitina a jam’iyyar PDP, kamar yadda Wasu labaran suka nuna.