Daga Walid Hari
Babban kamfanin mai na Najeriya NNPC ya bayyana samun gagarumar riba, da ya ce bai taba samun irinta ba a ‘yan shekarun da suka gabata.
Shugaban kamfanin, Mele Kolo Kyari, ya shaidawa manema labarai cewa a bana sun samu ribar naira biliyan 674, bayan asarar da suka tabka a shekarun da suka gabata.
Mista Kyari ya ta’allaka nasarar da suka samu kan sabbin sauye-sauyen da suka aiwatar a kamfanin, da suka hada da inganta hulda da abokan kasuwanci, da kuma kara sanya ido kan yadda lamura ke gudana a kamfanin.
Amma ya ce ya kamata a ce ribar ta zarta haka, ba don ba ta garin da ke fasa bututan man ba, da hakan ke janyo wa kasar asara makudan kudade.
Sai dai ya ce sun hada karfi da jami’an tsaron kasar don ganin sun yi maganin masu satar man da barnata dukiyar al’umma.