An dauki gabarar gudanar da bincike kan mutane hudu da suka mutu a jihar Kogi

Wasu Yan gida daya sun ce ga garin ku nan bayan lodan Amala da dare a jihar Kogi,

Rahotanni sun tabbatar cewa yanzu haka An kaddamar da bincike kan garin alabon da akayi amfani da shi wajen tuka tuwon Amalan wanda ake zargi yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu

Daga Kogi Al’ummar garin Mopa da ke karamar hukumar Mopa-Muro sun tashi da alhini tare da jimamin haɗi da makokin wasu ƴan gida daya su huɗu da suka hadu da ajalinsu bayan cin tuwon Amala.

Rahotanni da suke fitowa daga garin sun ce wadanda lamarin ya rutsa da wanda suka mutun ne a tsakanin ranar Juma’a 30 ga watan Satumba da kuma Lahadi 2 ga watan Oktoba na shekarar da muke ciki.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments