Kasar China ta kera jirgin Fasinja mafi kayatawa

Babban jirgin saman fasinja samfurin C919 da kasar China  ta kera, ya Sami  takardar shaidar da aka kera shi  wanda hakan ke nufin kasar ta China zata cigaba da kera jirgin mai samfurin C919.

Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin (COMAC), wanda ya kera jirgin na C919, ya karbi takardar shaida inganci daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta  kasar China (CAAC) dake da ofishi a yankin gabashin kasar.

A shekarar 2017 jirgin saman ya kammala gwajin tashinsa na farko cikin nasara, ya kuma samu irin wannan takardar shaida a karshen watan Satumba, abin da ke nuni da cewa, tsarin na C919, ya dace da mizanin tashi da kuma ka’idoji na muhalli.

A watan Maris din wannan shekara ce, kamfanin jiragen sama na China Eastern Airlines (CEA), ya sanya hannu kan kwangilar sayen jiragen na C919 guda 5, wannan shine  farkon kulla kasuwanci tsakanin kamfanonin biyu

Sakataren hukumar CEA Wang Jian, ya bayyana cewa, ana sa ran mikawa kamfanin na CEA jirgin farko a watan Disamba, za kuma a bayar da ragowar jiragen da aka yi oda a cikin shekara 1 ko biyu masu zuwa, bisa tsarin samar da jiragen.

Ana kuma sa ran kamfanin CEA, zai fara harkokin zirga-zirga da jirgin a cikin watanni 6 na farkon shekarar 2023.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments