Yajin aikin ASUU Saiti ne na jam’iyyar APC:Dan takarar shugaban kasa jam’iyar PRP

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP Kola Abiola, ya bayyana cewa za a kawo karshen yajin aikin da ke gudana na malaman ASUU watanni biyu kafin babban zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito  cewa Kola  ya magantu ne a wajen binne marigayi dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Ogun, David Bamgbos, ya ce yana takarar shugaban kasa ne don dakile tsarin rashin taimakon yan kasa.

A cewar sa gwamnatin tarayya za ta magance rikicinta da malaman ASUU ne  watanni biyu kafin zabe

Ya kara da cewa gwamnati za ta kawo karshen yajin aikin ne don dalibai da dama su samu damar yin zabe saboda zai zamana sun yi rijista ne a gida.

Dan takarar wanda ke rike da tutar Peoples Redemption Party ya kuma bayyana cewa yana nan a cikin tsaren shugaban kasa na 2023 don lashe zabe

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments