Wani tsohon mutum mai shekaru 93 da kuma wani likita mai shekaru 69 suna cikin jerin wadanda jami’an hukumar National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) suka kama yayin da suke kara kaimi wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi da kuma masu hannu a ciki a fadin kasar nan.
A daya daga cikin wadannan samame, an kama tsohon dattijo Pa Friday Ahukanna Chigbu mai shekaru 93 a gidansa da ke Umuagbaigba, kauyen Amavo Nkwogu, a karamar hukumar Osisioma ta jihar Abia, ranar Talata 7 ga Afrilu, 2026.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, an bayyana cewa binciken da aka gudanar a gidansa ya kai ga gano kilogram 7.7 na skunk, wani nau’in tabar wiwi (cannabis).









