Rundunar Sojojin Najeriya ta 17 Brigade da ke jihar Katsina State ta yi karin haske kan mutuwar wani soja, Cpl. Ude Jude, da ke karkashin rundunar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kyaftin Abayomi Adisa, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, ya fitar a ranar Lahadi a Katsina.
Adisa ya karyata rahotannin da suka yadu a kafafen sada zumunta da ke zargin an samu zagon kasa a cikin gida da kuma sakaci, yana mai cewa an kirkiro su ne da gangan domin yaudarar jama’a.









