Atiku Ya Nemi Adalci Bayan Harin Sama Ya Hallaka ‘Yan Kasuwa Sama da 50 a Iyakar Yobe da Borno

Atiku Ya Nemi Adalci Bayan Harin Sama Ya Hallaka ‘Yan Kasuwa Sama da 50 a Iyakar Yobe da Borno

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira da a tabbatar da adalci da daukar alhakin abin da ya faru, biyo bayan wani harin sama da ya afku a kasuwar Jilli da ke kan iyakar jihohin Yobe da Borno, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar ‘yan kasuwa marasa laifi sama da 50.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar a kasuwar Dilli da ke Jihar Yobe, kusa da karamar hukumar Gubio a Jihar Borno.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, ‘yan sa’o’i bayan aukuwar lamarin, inda ya ce abin da ya faru “ba wai abin takaici kadai ba ne, illa wata babbar gazawa ce mai tayar da hankali wadda dole ne ta fusata kowane mai hankali,” yana mai jaddada cewa rasa rayukan fararen hula yayin ayyukan soji abu ne da ba za a amince da shi ba.

“Yayin da ake kokarin kai hari kan ‘yan ta’adda, an sake mayar da ‘yan Najeriya marasa laifi hadaya. Har yaushe ne al’umma za su ci gaba da kasancewa cikin rashin tsaro, daga ‘yan ta’adda da kuma daga irin wadannan hare-haren da ake yi domin kare su?” in ji shi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments