Wata kotun tribunals da ke zaune a unguwar Ikotun a jihar Legas ta datse igiyar auren wasu maaurata sakamakon kama mijin da matar tayi turmi da tabarya da wata suna lalata a Otal.
A cewar matar mijin nata ya zaneta saboda yin korafi Kamar yadda matar ta sanar.
Tace mijinta mutum ne mai kwadayin abin duniya domin da mahaifiyarta ya dogara kuma itace take ciyar da su.
Alkalin kotun ya yi amfani da rashin halartar kotun da mijin yayi inda ya karbi bukatar matar na cewa a bata rainon yaran da suka haifa bayan datse igiyar auren.
Da take jawabi kan yadda ta kama mijin nata tace ta gan su dumu-dumu da wata mata suna lalata a dakin Otal, yayin da ta fuskance shi da maganar, ya nada mata duka.
Hakan yasa ta roki kotu da ta raba auren, saboda gudun ta cigaba da shan duka, da cin zarafi da rashin samun soyyaya da kulawa daga mijin nata.