Tsohon babban dogarin shugaban kasa na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-mustapha ya bayyana shirin sa na tarewa a sambisa idan har ya zama shugaban kasa, a cikin wata shida zai kawo karshen matsalar tsaro ta Boko Haram da ta addabi Najeriya.
Almustapha ya ce, zai je ya tare a dajin Sambisa, da ke jihar Borno, inda nan ne ake ganin matattarar mayakan Boko Haram, tsawon sati daya domin daukar duk matakin da ya wajaba a dauka domin ganin karshen mayakan.
Ya ce idan har ya zama shugaban kasa to lalle ne abin Allah ya shimfida za a yi wa dole ne a yi shi, ya ce, ”komai zafinsa a idon ko su waye”, yana mai bayar da misali da matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.
Ya nuna takaicinsa da damuwa kan yadda yake ganin sojojin Najeriya yanzu sun lalace ba su da kishi da kuzari kamar da, inda ya ce, ”Ka ga soja, duk sojan Najeriya ni ina ganinsa daidai yake da dan-sanda na da, saboda sun riga sun zama dan-sandan, kuma ‘yan-sandan da kuke da su sun gurbata, sun gurbata. Ni akwai abin da in zan yi a wata shida za ka ji tsoron abin da za a yi amma kuma shi ne gaskiya.”
Ya ce zai yi wa sojojin Najeriya garambawul a cikin wannan wa’adi na wata shida, wanda hakan abu ne da zai kasance da zafi amma kuma ya zama wajibi domin ya dawo da karfi da kuzarin sojojin Najeriya kamar yadda aka san su a baya.
”Misali ba shegantakar nan ta Boko Haram ba, wallahi ni zan ce a wata shida indai ba ta yi ba, duka manyan nan sai an rage muku girma, kuma za ku tafi gida, kuma za a hukunta ku kudin da aka ba ku sai kun fid da shi, sai an yi musu probe (bincike), a wata shida a matsayina na shugaban kasa zan je Zambiza can zan koma can zan yi hutu, zan yi hutun sati wurin in wani abu ya taba ni ma gani ” in ji shi.
Tsohon dogarin yana magana ne a hira ta musamman da BBC, inda ya bayyana shigarsa jerin masu neman takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a shekara mai zuwa ta 2003, inda zai nemi takara a karkashin jam’iyyar Action Alliance