Rahotanni na nuni da cewa Mayakan ISWAP sun kashe akalla kimanin mutane 30 a matsayin ramakon kashe kwamandan su da sojoji suka yi ta hanyar kai harin sama a Jihar Borno.
Majiyoyi daga yankin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa cewa mayakan sun kai hari ne a kauyen Mudu dake Yankin Dikwa.
Wani shugaban ‘Yan Sakai da ake kira Bakura Kolo ya bayyana cewa mayakan sun yanka akasarin mutanen da suka kama ne wadanda maza ne dake kokarin tserewa daga yankin.
Kolo yace akasarin wadanda aka kashe ’yan gwangwan ne dake neman karafa daga motocin da aka kona ko aka daina amfani da su a yankin saboda hare haren mayakan book haram bayan sun je kauyen daga Rann wanda ke da nisar kilomita 80 a tsakanin su.
Wani shugaban ‘Yan Sa Kan Umar Ari yace mayakan ISWAP sun zargin wadanda suka kashen ne da baiwa jami’an tsaro bayanai game da harkokin su.
Rikicin boko haram yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 40,000 da kuma raba mutane sama da miliyan biyu daga muhallin su tun daga shekarar 2009.