Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Hukumar hisbah ta jihar tasha alwashin yin duk mai yuwuwa wajan cigaba da horas da mata yadda zasu zauna lafiya da mazajensu.
Mataimakiyar kwamandan hukumar hisbah a Bangaren mata malama kulsum kasim ce ta bayyana hakan a yayin taron fadakarwa bisa wasu mahimman abubuwan da ya kamata mata su samu don aurensu yayi Danko wanda aka shiryawa mata yan’hisbah daga kananan hukumomin kwaryar binning Kano.
Malama kulsum tace gyaran aure abune da ya zama wajibi musammam ta yadda hukumar take cin karo da mas’a lolin ma,aurata ako da yaushe don haka sashen karkashin jagorancin Malama Hafsat isah waziri ta shirya wannan gagarumin bita don matan hukumar domin ko wane aikin alheri kyawunsa ya faro daga gida kafin a kaishi waje duk da cewar sashen ya dade yana wannan aiki a jihar Nan.
Malama kulsum ta kuma ja hankalin matan dake kano da sauran jihohin arewa dasu rungumi tsafta a gidajen aurensu.
Babbar bakuwa a wajen taron malama zainab jafar Mahmud Adam tayi bayani akan gyaran zuciya tace in zuciyar mata ta zama mai tsarki ba za,a samu kauce hanya ba a zaman aure.
Shugabar sashen gyaran auren malama hafsat isah waziri ta lasafto mahimman abubuwa uku da mata zasu kaucewa Dan zama lafiya da maza jensu wadanda suka hadar da zage _zage a cikin gida da tuhumar maigida da kuma binciken sa da cewa suna gurgunta aure.
Malama aisha Bala ta gyaran auren da malama Baraka.muhd Hassan sun fadawa matan wasu sirrukan mallakar miji. Taron ya samu hatattan manyam mata daga sassa daban daban na jihar nan.