Har yanzu Ina Tattauna Wa da Mambobin Jam’iyyar PDP da Suka Fusata Domin shawo kansu: Atiku Abubakar

Ina Tattauna Wa da Mambobin Jam’iyyar PDP da Suka Fusata Domin shawo kansu: Atiku Abubakar

ÆŠan takarar shugaban Æ™asa Æ™arkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace bai hakura ba har yanzu yana tattauna wa da mambobin da suka fusata domin shawo kan rikicin da ya addabi jam’iyyar.

Daily Trust ta tattaro cewa Atiku ya yi wannan furucin ne ne a jihar Gombe, jim kaÉ—an bayan buÉ—e sabon Ofishin da jigon PDP, Jamilu Isiyaku Gwamna, ya ba shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna alamun kwarin guiwa da cewa rikicin da ya Æ™i ci ya ki cinye wa za’a warware shi kuma PDP zata tunkari zaÉ“en 2023 da Æ™arfinta.

Alhaji Atiku ya Æ™ara da cewa har yanzun PDP shahararriyar jam’iyya ce kuma mafi daÉ—e wa a Najeriya, haka nan ita ke da damar lashe zaÉ“en shugaban Æ™asa da ke tafe a 2023.

“Mun gano cewa mun tafka kuskure kuma muna aiki ba dare ba rana domin gyara wannan kuskure, sannan muna da yaÆ™inin ‘yan Najeriya sun yi amanna da mu.”

“Yan Najeriya zasu iya kwatanta Æ™oÆ™arin mu da na abokan hamayya kuma ina da tabbacin banbanci a bayyane yake, haka zalika abinda muka yi kaÉ—ai ya isa ya wakilce mu.”

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments